minbarin duniya


4.3 ( 3273 ratings )
Utbildning Böcker
Utvecklare: fada media
1.99 USD

Manufar minbarin duniya shine isar da sakon asalin musulunci da yaren hausa, ta hanyar yada hudubobi da karatuttuka da takardu masu yawan gaske, da amfani da hanyoyin sadarwa kamar yanar gizo wadanda suka kunshi bidiyo, takardu, rediyo, da hotuna. Kamar yadda zamu yada su ta hanyar littafin koyarwa da tarbiya, bugu da kari kuma tare da tsara su a kan naurar nan mai muhimmanci). iPhone-iPod-iPad).
Minbarin duniya yana kunshe da fagage kamar haka :
1- Fagen imani: cikin abinda ya kunsa akwai [tauhidi, sharhin sunayen Allah kyawawa, dogaro ga Allah, aljanna da wuta, alamun tashin kiyama..da dai sauran su…}
2- Fagen zamantakewa: Daga cikin abinda ya kunsa akwai [ Biyyaya ga iyaye, girmamawar da musulunci yayi wa ya mace, zakka, yadda ya kamata ayi muamala da wadanda ba musulmai ba..da sauran su..]
3- Fagen yada daawa: Daga cikin abubuwan da ya kunsa akwai [ hanyoyin mallake zukata, da kwadaitarwa wajen neman ilimi da aiki da shi ...da dai sauran su..]
4- Fagen suluki: Daga cikin abubuwan da ya kunsa akwai: [ Tsoratarwa daga kurakuran harshe, tuba daga munanan ayyuka, hadarin mummunar shiga ga yaya mata, tasirin kayan maye ga samari, da mu}amalar banza tsakanin maza da mata...da dai sauran su...
5- Fagen ibada: Daga cikin abubuwan da ya kunsa akwai:[ Yadda ake kankan da kai wa Allah a sallah, tarbar watan ramadan, falalar goman karshe na zulhijja..dai dai sauran su...|
6- Fagen munasabobi: Daga cikin abubuwan da suka kunshi [ Babbar sallah, sallar rokon ruwa, sallar tsoro, sallar kisfewar rana da wata...da dai sauran su.....]
Duka wadannan abubuwa an sanya su a sigar takardu , da shirye-shiryen tibi da rediyo , kuma da sannu za a yada su ta yanar gizo da kafafen yada labarai na zamani ,kuma da sannu za a samar da cds masu kunshe da wdannan karatuttuka , na bidiyon su da na rediyon su da rubutattu su, kamar yadda dai za a watsa wadannan abubuwa ata satelite da gidajen rediyo dabandaban masu magana da harshen hausa.